Jami’an hukumar kula da shige da fici ta Najeriya, NIS ta kama wani dan kasar Amurka da makamai a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas.
Mutumin na da fasfon Najeriya da kuma na kasar Amurka, hakanan bai bayyana makaman da yake dauke dasu ba ga hukumomi.
Saidai an ga wasu takardu dake nuna cewa yana da izinin rike makaman wadda kasar Amurka ta bashi.
Amma ba’a kai ga tantance sahihancin wadannan takardu ba.