‘Yansandan Najeriya sun kama dan takarar Gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a jihar Rivers watau, Farah Dagogo.
Ana zargin Farah Dagogo ne da hannu a kai hari wajan tantance ‘yan takarar majalisar tarayya da na jiha na jihar Rivers din.
An kamashine da yammacin jiya, Alhamis bayan gwamnan jihar, Nyesome Wike ya zargeshi da hada hannu da matsafa da ‘yan ta’adda wajan kaiwa wajan da ake tantance ‘yan takarar hari.
Farah Dagogo dai dan majalisar wakilai ne kuma yana son tsayawa takarar gwamnan jihar Rivers din.
Saidai ya musanta zargin da ake masa.