fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Da Duminsa: An kama jami’an tsaro a cikin masu garkuwa da mutane a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa an kama wasu mutane na shirin kaiwa ‘yan Bindiga kudin fansa.

 

An kama Naira Miliyan 60 ne da ake shirin kaiwa ‘yan Bindigar dan kubutar da wanda suka sace.

 

Lamarin ya farune a yankin birnin gwari, kamar yanda PR Nigeria ta ruwaito.

 

Cikin wanda aka kama din akwai jami’an tsaro a cikinsu, saidai ba’a bayyana sojoji ne ko ‘yansanda ba.

 

An dai kubutar da wanda aka yi garkuwa dasu din inda kuma aka kashe wasu daga cikin ‘yan Bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.