Rahotanni daga kasar Jamus na nuna alamar cewa an kwantar da gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu a asibitin kasar.
Gwamnan ya bar Najeriya bayan halartar babban taron jam’iyyar APC a Abuja inda ya tafi kasar Jamus.
Daya daga cikin hadiman gwamnan ya amsa cewa lallai gwamman baya Najeriya, kamar yanda Sahara Reporters ta ruwaito.
Wasu ‘yan jihar ta Ondo dai tuni suka fara caccakar gwamnan kan wannan tafiya.