Rahotanni daga majiyoyi da yawa sun ce bayan harin da aka kai gidan yarin Kuje dake babban birnin tarayya, Abuja.
An nemi Babban dansanda, Abba Kyari an rasa inda ya shiga.
Lamarin ya tayar da hankula inda ake tunanin ko ya tsere ko kuma an saceshi.
Jaridar punchng ta bayyana cewa wasu ma’aikatan gidan yarin sun bayyana cewa har yanzu basu san inda Abba Kyari yake ba.
Wani yace bai fito sallar Asubaba kamar yanda ya saba fitowa ba.
Saidai da Jaridar Punchng ta tuntubi hukumar gidan yatin tace Kyari yana nan bai bata ba, tace kuma ba’a canja masa mazauni ba.
A rahoton jaridar The Nation kuwa, tace DCP Abba Kyari da abokan aikinsa da aka kama bisa zargin safarar kwaya sun tsere daga gidan yarin.
Hakanan rahoton The Nation ya kara da cewa, tsohon Gwamnan Taraba da Takwaransa na jihar Filato duk suma ana tunanin sun tsere.