Wasu dalibai mata hudu na kwalejin kimiyya da fasaha ta lafiya dake Tsafe a jihar Zamfara da aka sace a ranar Laraba 13 ga watan Afrilu sun samu ‘yanci.
Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki gidansu da ke wajen harabar makarantar da sanyin safiyar ranar inda suka tafi da daliban zuwa inda ba a san inda suke ba.
A jiya ne aka sako daliban matan bayan an biya kudin fansa naira miliyan daya. Majiyar ‘yan uwa ta ce iyayen daliban hudun da aka sace sun bayar da gudunmawar kudi naira 250,000 kowannensu domin hada kudin fansa.
Yanzu haka dai daliban na can a garin Tsafe kuma daga baya za a sada su da iyalansu.