An sako Daliban jami’ar Ahmadu Bello daga hannun masu garkuwa da mutane.
Babban jami’in tsaro na makarantar, Ashiru Zango ne ya tabbatar wa PREMIUM TIMES labarin a safiyar Lahadi.
“Ee, an sake su amma ina jiran samun cikakken bayani daga HOD dinsu wanda ke kula da tattaunawar,” in ji shi.
Mista Zango bai bayyana ko an biya wani kudin fansa ba don a sako su.
Duk da haka, wata jarida, News Express, ta ruwaito cewa an saki daliban ne a daren Asabar bayan an biya Naira miliyan daya a matsayin kudin fansa ga kowane daya daga cikinsu.
An sace daliban ne yayin da suke tafiya zuwa Legas domin wani shirin karatu. Wadanda suka sace su sun nemi a ba su Naira miliyan 270 a matsayin kudin fansa, kamar yadda jaridun Daily Trust suka ruwaito.
A cewar rahoton, Dickson Oko, daya daga cikin daliban da suka yi nasarar tserewa lokacin da lamarin ya faru a kan babban hanyar Abuja zuwa Kaduna, ya ce masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 30 a kan kowannensu.
Mista Oko ya yi nasarar tserewa tare da direban motar bas din a cikin daji amma abin takaici ya samu raunuka daga harbin bindiga.