fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Da Duminsa: An saki daliban Kagara

Rahotanni dake Fitowa daga jihar Naija na cewa an saki daliban makarantar sakandare ta Kagara da aka sace a jihar Naija.

 

Eonsintelligence ta ruwaito cewa an saki Daliban da sauran wasu da aka yi garkuwa dasu.

 

Dalibai da malamansu da wasu ma’aikatan Makarantar ne aka sace su kimanin 42. An dai baza sojoji da ‘yansanda wajan neman wadannan dalibai. Inda hadda jiragen yaki sai shawagi suke.

 

Dama dai Jami’an tsaro sun sanar da cewa sun gano inda aka boye daliban kuma sun wa wajan kawanya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *