Jam’iyyar me mulki ta APC ta tsayar da ranar 30/31 ga watan Mayu a matsayin ranar da zata yi zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa.
Hakanan ta tsayar da ranar 23 ga watan Mayu a matsayin ranar zaben fidda gwani na dan takarar gwamna.
Tuni dai jam’iyyar ta aikewa da hukumar zabe me zaman Kanta INEC da wannan aniya tata.