Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi barazanar tsawaita yajin aikin da ta ke yi nan da makonni biyu.
Hakan na zuwa ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke da INTEL REGION ta samu.
Kungiyar ASUU ta yi Allah-wadai da yadda Gwamnatin Tarayya ke tafiyar da tattaunawar wanda hakan yasa ba cinma matsaya ba.