fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Da Duminsa: Atiku na shirin kara daukar Peter Obi a matsayin mataikinsa amma wasu ‘yan PDP sun ce basu yadda ba

Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na shirin sake daukar Peter Obi a matsayin mataimakinsa wanda zasu yi takara tare a shekarar 2023.

 

Koda a shekarar 2019, Atiku da Peter Obi yayi takarar shugaban kasa wadda kuma ya samu kuri’u Miliyan 11.

 

Hakan ya bayyana karara saboda Peter Obi duk da ya fito takarar shugaban kasa amma ya halarti wajan taron da Atiku ya bayyana cewa zai fito yakarar shugaban kasa.

 

Wata majiya me karfi ta gayawa jaridar Independent cewa, Atiku zai dauki Peter Obi ne saboda yafi yadda dashi kuma sun yi aiki tare a baya.

Karanta wannan  Mutane miliyan daya muka kashe domin a samu zaman lafiya a Najeriya, cewar shugaba Buhari

 

Saidai wasu ‘yan PDP, musamman gwamnoni basu yadda da wannan tsarin ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.