Dan majalisa James Faleke da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da magoya baya da yawa sun je sun saiwa Bola Ahmad Tinubu fom din takarar shugaban kasa na Miliyan 100 na jam’iyyar APC.
Sun sayi fom dinne karkashin wata kungiya me goyon bayan Tinubu da ake kira da TSG a takaice.