fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Da Duminsa: Bafa zan saki Nnamdi Kanu ba>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ba zai saki shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ba.

 

A baya dai dattawan Inyamurai sun kaiwa shugaba Buhari ziyara inda suka nemi ya saki Kanun, amma a ganawar da aka yi dashi a Channels TV,  yace shi fa ba zai yi katsalandan ga shari’ar da akewa Kanu ba.

 

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, an baiwa Nnamdi Kanu damar ya kare kansa a kotu kan zargin da ake masa, amma ba zai sakeshi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.