Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, wani bam da ‘yan Bindiga suka dasa ya tashi da hatsabibin dan Bindiga, Dogo Gudali inda ya mutu.
Rahoton yace, yaran dan bindigar ne suka dasa bam din daya kasheshi.
Wani jami’in soja ya bayyana cewa ‘yan Bindigar sun dasa bam dinne dan kashe sojoji.
Rundunar soji dai ta Hadarin Daji na kan bibiya da kakkabe burbushin ‘yan Bindigar.