Ofishin dake neman ganin tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa a shekarar 2023 ya bayyana cewa basu san da maganar fitar da dan takarar shugaban kasa na bai daya ba a jam’iyyar PDP.
Kungiyar dattawan Arewa ta fitar da tsohon kakakin majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki da Gwamnan jihar Bauchi a matsayin gwanayen Arewa a zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Professor Ango Abdullahi ne ya jagoranci bayyana ‘yan takarar.
Saidai tuni gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal dake tare da kungiyar a baya, ya fito ya bayyana cewa bai san da wannan maganar ba.
Hakanan shima kwamitin dake kula da fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa bai san da wannan magana ba.
Shima tsohon Mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa bashi da alaka da fidda wannan dan takarar.
Atiku yace ba’a taba samun rarrabuwar kan ‘yan Najeriya irin a wannan lokaci da muke ciki ba, kuma irin wannan tsari na fitar da dan takara, zai kara raba kan kasar ne kawai.
Mu fatan mu kwankwaso ya Zama shugaban kasa in Sha Allah a 2023
Wannan gaskiya ne Mai gidan atiku