fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Da Duminsa: Birtaniya ta amince da gwamnatin Nageriya da ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar yan ta’adda

A karshe dai kasar Birtaniya ta durkusa wa Najeriya inda ta amince da haramta kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) a matsayin kungiyar ta’addanci, shekaru biyar bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta’addanci a Najeriya.

Matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka na amincewa da kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci ya fito ne a cikin wata sabuwar sanarwa kan mafakar da ta fitar ta hanyar Visa da Shige da Fice ta Burtaniya (UKVI) a shafinta na intanet.

Manufofin da aka sabunta a watan Mayu 2022 ta ce ta amince da gwamnatin Najeriya wacce ta sanya kungiyar IPOB da kungiyar ta ‘yan ta’adda, Eastern Security Network (ESN) a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe 'yan sanda biyu, sun jiwa biyar rauni a jihar Borno

Gwamnatin Birtaniya ta kuma zargi IPOB da ESN karkashin jagorancin Nnamdi Kanu da aka kama da laifin yawaitar tashe-tashen hankula da take hakin bil’adama a yankin Kudu maso Gabashin kasar, inda ta umarci jami’anta na biza da su cire ‘ya’yan kungiyar daga shirinta na neman mafaka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.