Jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce Najeriya na bukatar shugaba irinsa mai jajircewa wajen aiwatar da sauye-sauyen da za su kawo kudaden shiga da gina kasa.
Ya bayyana kansa a matsayin mutumin da Najeriya ke bukatar domin kawo harkokin ci gaba a kasar.
Tinubu yayi magana ne a wajen taron kwana daya tsakanin shuwagabannin majalisar wakilai da mataimakansu na Jihohin da APC ke jagoranta.
Ya kara da cewa, duba da halin da kasar ke ciki akwai bukatar shugaba mai sadaukarwa da gwazo domin magance matsalolin kasar.