Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa an tafka kazamin fada tsakanin Bello Turji wanda shahararren dan Bindiga ne da kuma wata kungiyar ‘yan Bindigar ta daban.
Rahoton yace, Turji ya kaiwa sansanin Dullu da Dan Maigari, Hari inda kuma ya kashesu tare da wasu mabiyansu 15.
Lamarin ya faru ranar Talata da safe kamar yanda Daily Trust ta ruwaito inda tace wannan fada shine mafi muni da ya faru tsakanin ‘yan Bindigar wanda suka dade basa ga maciji a tsakaninsu.
Rahoton yace Turji da mutanensa sun kaiwa bangarwn Dan Maigari da Dallu harin kwantan baunane inda suka musu kisan kare dangi.