fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Da Duminsa: Dan Kunar Bakin Wake ya kashe mutane 50 a wani mummunan hari

An ji karar abin fashewa mai karfin gaske a wani masallaci da ke yammacin birnin Kabur na Afhanistan a lokacin da ake yin sallar juma’a.

Jami’an Afghanistan sun ce akalla mutane 50 ne suka mutu a wannan hari, wasu da dama kuma suka ji mummunan rauni.

Mai magana da yawun ma’aikatar cikin gida Besmullah Habib, ya ce an kai harin ne masallacin Khalifa Shib da ke Kabul.

Tun farkon azumin watan Ramadan ake zafafa kai hare-hare a wuraren ibada da taruwar jama’a a Afghanistan.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari na ranar Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published.