Fada ya barke a dajin Sambisa tsakanin Kungiyar Boko Haram da wadda ta balle daga cikinta, ISWAP.
Hakan yayi sanadiyyar kisan mutane akalla 32 a cikin kungiyoyin 2.
Zagazola Makama ya bayyana cewa hare-haren sun farune a Yale in Damboa da Gargash dake yankin Bama.
Boko Haram ce ta fara kaiwa ISWAP harin kwantan bauna a kauyen Yale ranar 19/April/2022.
Sun kama ‘yan ISWAP 4 inda suka kwace makamansu suka kuma musu yankan rago.
Boko Haram ta kuma yiwa ISWAP kwacen motoci 3.
Hakana wata majiya daga gidan soja itama ta tabbatar da cewa fadan na Boko Haram yayi sanadiyyar mutuwar mutane 18 daga cikin kungiyar.