Akalla mutane 4 ne suka mutu a wani harin ramuwar gayya da ake zargin Fulani sun kai a Agbon Ojodio dake Yewa a jihar Ogun.
Lamarin ya farune ranar Lahadin data gabata da yamma. Kuma yana zuwa ne bayan na ranar Juma’ar data gabata da aka kai Ebuta Igbooro da shima aka kashe mutane 4 da na ranar Alhamis a Owode Ketu wanda shi kuma aka kashe wasu 6.
A wannan yankin ne dai aka kaiwa Fulani Makiyaya hari wanda ake zargin Sunday Igboho da tunzurawa inda aka koresu aka lalata musu dukiya, kwanaki kadan da suka gabata.