fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Da Duminsa: Gwamnan Najeriya ya fallasa masu daukar nauyin ta’addanci da kuma dalilin da yasa suke hakan

Gwamman jihar Cross-Rivers, Ben Ayade ya bayyana masu daukar nauyin ta’addanci a Najeriya inda yace suna yi ne dan hana kasar ci gaba.

 

Yayi wannan tonon Silili ne a hirar da aka yi dashi q Channels TV inda yace kasashen yamma ne ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya.

 

Yace babbar kasuwar kasashen yamman itace Africa inda suke kawo kayansu suna sayarwa dan haka ne ba’a son Africa ta samu zaman lafiya yanda ci gaba zai zo mata.

 

Yace ya kamata Najeriya ta koma aiki da kasashen Turkiyya da Israel wands yace su basu amfana da matsalar tsaron da ake fama da ita.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published.