Majalisar iyayen kasa a zaman da ta yi na yau a fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta amince da yafewa tsohon gwamnan Taraba, Rev. Jolly Nyame laifin da yayi wanda yasa yanzu haka yake daure a gidan yari.
An daure tsohon Gwamnan ne saboda Almundahanar kudi da aka sameshi da ita lokacin yana gwamna.
Jolly Nyame ya mulki jihar Taraba daga shekarar 1999 zuwa 2007.
Tuni majalisar ta aikawa babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma ministan shari’a Abubakar Malami bukatar sakin Jolly Nyame wanda shi kuma zai aikewa gidan yarin da suke tsare da tsohon gwamnan dan su sakeshi.
A watan Fabrairu na shekarar 2020 ne dai kotun koli ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 12 ga gwamnan.