Gwamnatin tarayya ta ware ranekun 2 da 3 ga watan Mayu watau, Litinin da Talata a matsayin ranekun hutun Sallah da ranar ma’aikata.
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka ta bakin sakatariyar ma’aikatarsa, Shuaib Belgore.
Sanarwar ta ranar Alhamis ta jinjinawa Ma’aikatan Najeriya inda ministan yace aikin da suke tukuru ne yasa Najeriya ta yi zarra a tsakanin kasashen Duniya.
Ya jawo hankalin ma’aikatan su ci gaba da aiki tukuru dan ci gaban kasa.