Alamu sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta fara daina biyan malaman jami’a dake yajin aiki karkashin kungiyarsu ta ASUU.
Dama dai gwamnatin tarayyar ta yi barazanar daina biyan malaman albashi saboda yanda basa aiki.
Kungiyar ta ASUU ta bayyana cewa, tana ta aikawa gwamnatin tarayya takarda kan maganar yajin aikin amma gwamnatin taki kulawa ta dauki matakin da ya dace.
Daya daga cikin Shuwagabannin ASUU, Comrade Ibeji Nwokoma ya bayyana cewa, membobinsa ba’a biyasu cikakken Albashin watan Maris ba.
Saidai ya gayawa jaridar Vanguard cewa, dakatar da albashinsu ba zai hana su ci gaba da yajin aikin ba, saboda gyara suke son kawowa.