Gwamnatin tarayya zata gana da kungiyar malamin jami’a, ASUU kan yajin aikin da kungiyar take.
Ministan kwadago, Chris Ngige ne zai gana da malaman, Kwanaki 56 bayan fara yajin aikin malaman.
Da misalin karfe 5 na yammacin yaune ake sa ran fara zaman.
ASUU na neman gwamnatin ta biya mata bukatunta da suka hada da biyan Alawus-Alawus, da fara Amfani da tsarin UTAS, da kuma bayar da kudin gyaran jami’o’in Najeriya.