fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Da Duminsa: Hukumar Hisbah ta kama kwalabe 1,426 na barasa a jihar Jigawa

Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta kama kwalabe 1,426 na barasa iri-iri a kananan hukumomi biyu na jihar.

Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Dutse ranar Alhamis.

Dahiru ya ce rundunar ta kuma kama wani jeri mai lita 25 na barasa, wanda aka fi sani da “burukutu”.

Ya bayyana cewa an kwace barasa ne a lokacin da jami’an Hisbah suka kai samame a otal-otal da wuraren shan barasa da kuma wuraren da abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.