Me shugabantar yiwa Bola Tinubu yakin neman zabe a jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya fice daga jam’iyyar APC.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta.
Yace ya yiwa APC iya abinda zai iya kuma lokaci yayi da ya kamata ya canja sheka.
Saidai be bayyana jam’iyyar da zai koma ba amma yace nan da awanni 24 zai sanar da inda ya koma.