Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano (PCACC) Ta bayyana cewa, General Idris Bello Dambazau Me murabus da take tuhuma kan zargin satar kudi ya tsere daga hannunta.
Dambazau shine shugaban hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki ta jihar Kano kuma ana tuhumarsa da zargin Rashawa da cin hanci.
Shugaban riko na hukumar ta yaki da rashawa ta jihar Kano, Barrister Màhmoud Balarabe ya bayyana cewa ana kan yiwa janar Dambazau tambayoyi shine yace bari ya je gida ya sha maganinshi.
Ma’aikatan hukumar sun rakashi gidan nasa amma anan ya musu batan dabo suka rasa inda ya shiga.
Yace dama kamin fara masa tambayoyin sai da aka kai ta fama dashi ya amsa gayyatar da ake masa amma yaki, daga baya ne da yaji an ce za’a kamashi ta karfin tsiya sai ya amince.
Ko da a shekarar 2021, saida hukumar DSS ta kama Dambazau amma daga baya aka sakeshi ba tare da cewa ya aikata laifin komai ba.