Kungiyar Al-Nasr dake kasar Saudiyya ta kammala sayen dan wasan kasar Portugal, Cristiano Ronaldo akan Fan Miliyan 173.
Kafar Marca tace, Ronaldon zai saka hannu akan yarjejeniyar bugawa Al-Nasr wasa a watan Janairu.
Rahoton yace, kudin da suka kusa Fan Miliyan 200 na Ronaldon sune na gaba-gaba a tarihin kwallon kafa da aka taba sayen dan wasa.