Kungiyar Ansaru ake karkashin kungiyar Boko Haram ta fara jan ra’ayin matasa dan shiga cikinta.
Lamarin na faruwa ne a Birnin Gwari dake jihar Kaduna.
Dailypost ta ruwaito cewa, kungiyar ta Ansaru a kokarin jawo hankalin matasan ta rika raba kayan Sallah da sauran kayan amfanin rayuwa.
Wani mazaunin yankin, Alhaji Usman Dankabo ya bayyanawa kafar cewa kungiyar ta je kauyukan Damari, Farin Ruwa, Kwasa Kwasa, Kuyello, Gobirawa, Tabanni, Kutemeshi da Kazage, dan neman matasa da zata dauka su shiga cikinta.
Yacs bayan kayan amfanin da suke rabawa suna kuma yiwa mutane wa’azi.