fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Da Duminsa: Kungiyar Boko Haram ta kaiwa tawagar Gwamnan Borno hari

Rahotanni dake fitowa daga jihar Borno na cewa, Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram ta kaiwa tawagar Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum hari.

 

Tawagar na tafiyane daga Baga zuwa Maiduguri yayin da mummunan harin ya faru.

 

Kungiyarce da kanta ta fitar da sanarwar hakan inda tace ta kashe mutane da yawa.

 

Saidai babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Bornon a hukumance data tabbatar da wannan ikirari na kungiyar.

Sannan babu cikakken bayanin ko gwamna Zulum na cikin tawagar motocin yayin da aka kai harin ko kuwa.

Karanta wannan  Kalli hotunan 'yan damfara da aka kama a jihar Bauchi

 

A baya dai kungiyar tasha kaiwa tawagar gwamnan hari amma yana tsallakewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.