fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Da Duminsa: Kungiyar gwadago, NLC zata fara yajin aiki tace sai gwamnati ta sasanta da ASUU sannan an magance matsalar tsaro

Kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana cewa, zata fara yajin aikin gargadi na kwanaki 3 saboda gazawar gwamnati wajan sasantawa da kungiyar malam jami’a ta ASUU.

 

Kungiyar a kwanakin baya ta baiwa gwamnati wa’adi kan ta sasanta da kungiyar malaman ta ASUU.

 

Amma gwamnatin bata yi wannan sasantawar ba.

 

Hakan ya tilasta NLC daukar wancan mataki.

 

Ta kuma ce tana neman gwamnati ta magance matsalar tsaro da kuma kubutar da wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane, da magance sauran matsalolin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.