fbpx
Friday, May 27
Shadow

Da Duminsa: Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta fadawa shugaba Buhari abin da suke so ya yi wa Nnamdi Kanu, da sauran masu fafutukar kafa kasar Biafra da aka kama

Kungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta bayyana wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari abin da suke so ya yi wa Nnamdi Kanu da sauran masu fafutukar kafa kasar Biafra da ke tsare a hannun gwamnatin tarayyar Najeriya.

Shugaban kungiyar Ohanaeze, Ambasada George Obiozor, ya roki shugaban kasar da ya saki Nnamdi Kanu, da dukkan matasan kabilar Ibo da ake tsare da su saboda neman kafa kasar Biafra.

George ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron Imeobi na Ohanaeze da ke gudana a sakatariyar Ohanaeze ta kasa a Enugu.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Peter Obi ya janye ra'ayinsa na tsawa takarar shugaban kasa kuma ya fice daga jam'iyyar PDP

Dangane da matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, shugaban kungiyar Ohanaeze ya bayyana fatansa na ganin cewa al’ummar Igbo za su fito da karfinsu domin kafa kasar Biafra.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.