Kungiyar dake neman kafa kasar Biafra ta IPOB, tace kwanannan zata fito da sabon salon yakin neman kafa kasar Biafra.
Kungiyar ta zargi jami’an tsaron Najeriya da suka hada da DSS, Army, Police, NSCDC da kuma wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama da yi mata karya.
Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin tarayya da jami’an tsaro cewa sune ke da alhakin matsalolin tsaron da ake fama dasu.
Sakataren yads labarai na kungiyar, Emma Powerful ne ya bayyana haka, kamar yanda the Nation ta ruwaito.
Kungiyar tace an yi taro dan a bata mata suna amma hakan ba zai kai ga nasara ba dan zama ta fito da sabon salon yakin neman kafa kasar Biafra ne.