fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Da Duminsa: Manchester United ta amince da sayar da Cristiano Ronaldo, Ya fara tattaunawa da Barcelona

Rahotannin dake fitowa daga Ingila na cewa, Manchester United ta amince da sayar da babban dan wasanta, Cristiano Ronaldo.

 

Ronaldo dai na neman barin kungiyar amma da farko ta ki amince masa, saidai sabbin rahotanni sunce a yanzu kungiyar ta amincewa Ronaldo ya tafi.

 

Saidai kungiyar tace ba zata sayarwa daya daga cikin kungiyoyin Premier league Ronaldon ba.

 

An samu rahoton cewa, Wakilin Ronaldon, Jorge Mendes yayi ganawar sirri da kungiyar Chelsea a kokarinta na sayen Ronaldon.

 

Saidai a wani sabon rahoton kuma, wakilin Ronaldon, Jorge Mendes zai yi kokarin komawar dan wasan me shekaru 37 Barcelona.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.