Rahotannin dake Fitowa daga Jihar Kano na cewa masu a daidaita Sahu sun amince da biyan Harajin Naira 100 a kullun da Gwamnatin jihar ta saka musu.
Shugaban Kungiyar Gwadago na jihar, Kabiru Ado Minjibir ne ya bayyana cewa ana tsammanin masu adaidaita Sahun zasu ci gana da biyan kudin harajin.
Shima Daraktan KAROTA, Baffa Abba Dan Agundi ya bayyana farin cikinsa da wannan hadin kai na masu Adaidaita Sahun, kamar yanda DailyvNews24 ta Ruwaito.