Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da yin sulhu da haramtacciyar kungiyar IPOB.
Ya bayyana hakane a yayin ganawar da shugaba Buhari yayi da dattawan kudu maso gabas a ziyarar kwanaki biyu da shugaban kasar ya kai jihar.
Yace za’a tuna da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya taimakawa al’ummar Inyamurai.
Ya kuka nemi dattawan yankin su bada hadin kai wajan tabbatar da zaman lafiya a yankin.