Shugaban kungiyar IPOB dake tsare a hannun gwamnatin tarayya, Nnamdi Kanu ya bayyana cewa shi ba dan IPOB bane.
Lauyan dake wakiltar gwamnati a shari’ar da ake da Kanu, Shuaibu Labaran ne ya bayyana haka.
Kanu kuma ya musanta duka zarge-zargen da gwamnatin tarayyar ke masa.
Lauyan yace amma suna kokarin ganin sun tabbatar da tuhumr-tuhumen da akewa Kanun ta hanyar samar da shaidu da hujjoji.