Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin bude rumbun gwamnati a debo hatsi a rabawa ‘yan Najeriya.
Ministan noma da ci gaban karkara, Dr Mohammed Abubakar ne ya bayyana haka bayan ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja.
Ministan yace shi da ma’aikatar kula da ibtila’i da jin kai ne zasu yi aikin inda yace tan 40,000 ne shugaban kasar yace a debo a rabawa ‘yan Najeriya.
Ministan yace a shekarar 2020 lokacin cutar Coronavirus, shugaban kasar ya bayar da irin wannan umarni inda aka debo tan 70,000 aka rabawa ‘yan Najeriya.
Yace wannan kokarin shugaban kasa ne na rage wa ‘yan Najeriya radadin tsadar farashin kayan abinci da ake fuskanta.
Yace suna da Dawa, Gero, da Masara wanda suna runbunan dake ajiye a fadin kasarnan.
Za’a raba wannan hatsi ne a jihohin Najeriya gaba daya hadda babban birnin tarayya, Abuja.