fbpx
Monday, August 8
Shadow

Da Duminsa: Sojoji bakwai suka mutu ’yayin da Boko Haram sanye da kayan sojoji suka yaudaresu

Mayakan Boko Haram sun kashe a kalla sojoji bakwai a garin Doska da ke jihar Borno, kamar yadda majiyar sojojin suka shaida wa TheCable.
An ce sojojin suna cikin sintiri ne zuwa yankin lokacin da maharan suka yaudare su wadanda suka bayyana a cikin kayan sojoji da motocin daukar bindiga.
Doska, wani kauye da ke tsakanin Ajigin da Talala a karamar hukumar Damboa ta jihar, ya zama babu kowa tun daga shekarar 2015 lokacin da masu tayar da kayar bayan suka kwace yankin wanda har yanzu ya kasance daya daga cikin wuraren da suke da karfi.
“Sojojin suna cikin sintiri ne kuma a lokacin da suka isa Doska, sun ga wadannan mutane cikin kakin soji da injunan soja, har ma suna daga hannu don haka sojojinmu suka zaci sojoji ne daga wani sansanin,” in ji wata majiya.
“Sojojin sun tsaya, sun yi musabaha da wadannan mutane. Kuma suna cikin tafiya sai suka ci karo da ‘yan kwanton bauna, Nan take, maharan suka rufa musu baya, suna bude wuta.
“Mun rasa sojoji bakwai, sannan 14 sun samu munanan raunuka.”
Wata majiyar ta ce an san maharan a yankin koyaushe suna yi wa sojoji kwanton bauna da nufin sace motocin daukar bindiga da sauran makamai daga sojojin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan bindiga sun kashe 'yan vigilanti guda biyu sunyi garkuwa da wasu amare a jihar Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published.