fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Da Duminsa: Sojojin Najeriya na can suna barin wuta da ‘yan Bindiga

Rahotanni dake fitiwa daga garuruwan Orlu dake karamar hukumar Orsu ta jihar Imo na cewa, sojojin Najeriya na can suna barin wuta da ‘yan Bindiga.

 

Tun a daren ranar Asabar aka fara barin wutar wanda yasa mutane suka rika gudu dan neman wajan buya da ransu.

 

Sojojin sun samu bayanan sirri ne na cewa, ‘yan Bindigar suna taruwa a wajan da niyyar kai musu hari shiyasa su suka rigasu suka kai musu harin bazata.

 

An dai samu asarar rayuka amma ba’a kai ga jin na sojojin ne ko kuwa na ‘yan Bindigar ba.

Karanta wannan  Sakamakon jarabawata ta WAEC ta bata amma tayi matukar kyau don ni ne dalibi na biyu dayafi kokari a shekarar, cewar mataimakin Atiku, Okowa

 

Zuwa yanzu dai hukumar ‘yansandan jihar bata fitar da sanarwa ba kan lamarin, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.