Jami’an ‘yan sandan Soji na Division 81 ne suka damke sojojin na jabu a lokacin da ake gudanar da aikin tantancewar a jihohin.
Janar Ofisa Kwamanda (GOC) Division 81, Manjo Janar Umar Thama Musa ya ce sojojin na bogi ne ke aikata laifuka da dama.
Wata sanarwa a ranar Laraba 13 ga watan Afrilu, ta hannun mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar Soji ta 81, Manjo Olaniyi Joseph Osoba, ta ce wadanda ake zargin suna batawa sojojin Najeriya suna.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya ta 81 (GOC) ta 81 ta Sojojin Najeriya (NA) Manjo Janar Umar Thama Musa a wata ganawa da manema labarai ya yi watsi da labarin mara tushe na cewa duk wasu haramtattun ayyuka da masu sanye da kakin soji ke aikatawa a koda yaushe jami’an soji ne.
Hukumar ta GOC ta ce za a mika su ga ‘yan sandan Najeriya domin daukar mataki.
Don haka ya bukaci jama’a da su daina sanya kakin soja, riga, wando ko laka wata takarda da ta shafi soja a mota ko babur domin za su dauki mataki akan duk wanda suka kama.



