Tsohon gwamnan Legas, kuma jigo a jam’iyyar APC me son tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023, Bola Ahmad Tinubu yawa Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo shagube akan fitowa takarar shugaban kasa da Osinbajo yayi.
Tinubu yayi shaguben ne bayan ganawa da gwamnonin APC a Abuja.
Tinubu yace dalilin ganawar tasu shine fan ya nemi goyon bayan jam’iyyarsa ta APC kan takararsa ta shugaban kasa.
Da aka tambayeshi me zai ce kan dansa, Osinbajo da ya tsaya takarar shugaban kasa?
Sai ya kada baki yace ai bai da dan da yayi girman da zai tsaya takarar shugaban kasa.