Tsohon Sanatan Najeriya, Francis Arthur Nzeribe ya rasu a wani asibiti a kasar waje a ranar Lahadi 8 ga Mayu, 2022.
Sanatan wanda ya wakilci mazabar Sanata Orlu a jihar Imo a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.
A cewar majiyoyin da suka tabbatar da mutuwarsa, Nzeribe ya rasu ne a wani asibiti a kasar waje sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba.