Shugaban jam’iyyar APC na mazabar Ponyan dake jihar Kogi, Bunmi Ipinnaiye, ya kashe kansa.
An kamashi da zargin yunkurin kashe dansa wanda ya sassara da adda a hanyarsu ta zuwa gona.
Ko da aka kamashi yaki amsa tambayoyin da ake masa. Saidai daga baya an sameshi a inda ake tsare dashi ya kashe kansa.