Wani gini me hawa biyu dake titin Chris Igadi a Legas ya rushe a yau, Asabar.
Saidai an yi sa’a mutanen dake cikin ginin sun tsere bayan da ginin ya nuna alamar rushewa.
Babban sakarare a ma’aikatar bada agajin gaggawa ta jihar Legas, Dr. Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da cewa babu wanda ya jikkata a rushewar ginin.