Wani ma’aikacin gwamnati me suna Bala Musa ya maka tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon a kotu wai saboda ta ki aurensa.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ne ya tabbatar da hakan.
Hadizar da wanda ke zarginta sun je gaban kotun shari’ar Musulunci dake Kaduna a ranar Litinin.
Musa yacw sun dade suna soyayya da Hadiza Gabon kuma ta mai alkawarin aure.
Yace ya kashe kudi Naira 396,000 a kanta saboda duk kudin da ta tambayeshi yana bata sabosa tace zata aureshi.
Lauyan Hadiza Gabon, Mubarak Kabir ya nemi a bashi karin lokaci kamin ya kai Hadiza Gabon a gaban kotun kuma Alkalin ya saka ranar 13 ga watan Yuni a matsayin ranar da za’a ci gaba da shari’ar.