‘Yan Bindiga a jihar Delta sun budewa dan majalisar jihar, me wakiltar Ughelli South, Reuben Izeze wuta.
Saidai ya tsallake rijiya da baya bau mutu ba.
Lamarin ya farune a ranar Alhamis amma cikin sauri jami’an tsaro suka kai masa dauki, ba’a kasheshi ba.
Ya bayyana cewa, ya godewa Allah da tsallake yunkurin kisan da aka masa.