‘Yan Bindiga sun kashe Adamu Aliyu Wanda shugaban kungiyar Miyetti Allah ne dake Gwagwalada, babban birnin tarayya, Abuja.
An kasheshi ne tare da wasu mutane a kauyen Daku dake yankin Dobi na karamar hukumar a ranar Alhamis.
Sakataren kungiyar Miyetti Allah Mohammed Usman ne ya tabbatarwa da Daily Trust hakan inda jace an sace mutane 3 wasu 3 kuma sun jikkata.
Jami’an tsaron sojoji, ‘yansanda dana NSCDC sun halarci wajan kamin aka yi jana’izar wadanda aka kashe din.